Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomole da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a wata ganawar sirri da suka gudanar a fadar sa da ke Abuja.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, jiga-jigan jam’iyyar sun isa fadar shugaban kasa ne da yammacin ranar juma’ar da ta gabata, rana, inda nan ta ke suka zarce kai tsaye zuwa ofishin shugaban kasa, suka kuma garkame kofa.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, babu wanda ya san dalilin zuwan gwamnan da kuma shugaban APCn wajen Buhari, sai dai masana na ganin ziyarar bata rasa nasaba da zaben gwamnan jihar Kogi da ke karatowa.
Idan
dai ba a mantaba, a ranar 29 ga watan Agusta ne gwamna Yahaya Bello ya lashe
zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, inda
ya doke ‘yan takara fiye da biyar.