Jam’iyyar PDP ta yi wa Bola Ahemd Tinubu raddi, bisa zargin sa da furka wasu kalamai da ba su dace ba a kan ta, inda ta ce Tinubu ya na sukar ta ne don neman suna kamar yadda kakakin ta Kola Ologbondiyan ya bayana a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce ganin yadda Tinubu ya je kasa mai tsaki a cikin watan azumi dom kawai ya gana da shugaba Muhammadu Buhari, hakan ya nuna cewa APC ba ta san inda ta sa gaba ba.
Kola Ologbondiyan, ya ce abin kunya ne a ce lokacin da ake kokarin yi wa Nijeriya addu’a a kasa mai tsaki, amma babu abin da ya Tinubu illa bakar siyasarsa da kuma zagin jama’a don ya burge shugaba Buhari. Ya ce babu abin da zai kai Tinubu kasar Saudiyya ya na fadin irin kalaman da ya furta na yabon gwamnatin APC da ta gaza sai tsugudidi, kuma ya yi hakan ne don guje wa barazanar da wasu ke yi na tona asirin sa a fadar shugaban kasa.