Home Home Galibin Motocina Da Aka Kwashe Na Mallake Su Tun Kafin In Zama...

Galibin Motocina Da Aka Kwashe Na Mallake Su Tun Kafin In Zama Gwamna – Matawalle

82
0

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, ya ce galibin motocin da jami’an tsaro su ka kwashe daga gidajen sa da ke Gusau da Maradun ya mallake su tun kafin ya zama gwamna.

Matawalle ya bayyana haka ne, yayin da ya ke maida martani game da mamaye masa gidaje da ‘yan sanda da jami’an DSS su ka yi. Inda ya zargi jami’an tsaron da kwashe kayan matan sa da na yaran sa ciki har da suturun su.

Ya ce babu wani umarnin kotun da aka isar masa na halasta wa jami’an tsaron shiga gidajen sa kamar yadda magajin sa Dauda Lawal ya yi iƙirari.

Matawalle ya kara da cewa, motocin da aka kwashe a gidan sa na Maradun abokan arziki ne su ka ba shi gudunmawa, kuma baki ɗayan su su na ɗauke da hoton sa tare da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Ya ce ya kamata jami’an tsaro su bayyana motoci 40 da su ka ce sun gano a gidajen sa kamar yadda su ka yi iƙirari domin jama’a su gani su kuma yi alƙalanci.

Leave a Reply