Home Labarai Furta Kalamai: Barcelona Ta Kori Kocin Ta Xavi Hernandez

Furta Kalamai: Barcelona Ta Kori Kocin Ta Xavi Hernandez

111
0
2153286826.0
2153286826.0

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta sallami kocinta Xavi Hernandez bayan kammala kakar wasan bana ba tare da lashe kofi ba.

A gefe guda kuma, tsohon kocin Jamus Hansi Flick na gab da maye gurbin sa.

Xavi zai bar Barcelona ne bayan wasan da ƙungiyar za ta yi da Seviilla a ranar Lahadi, wanda shi ne na ƙarshe a kakar bana.

Xavi mai shekara 44 ya saka hannu kan yarjejeniya har zuwa 2025, amma an faɗa masa matakin da ƙungiyar ta ɗauka bayan ganawar shugabanta Joan Laporta da daraktan ƙwallon ƙafa Deco ranar Juma’a.

Sanarwar ta zo wata ɗaya daidai daga lokacin da aka sanar cewa Xavi zai ci gaba da zama a kulob ɗin.

Tsohon ɗan wasan tsakiyar na Sifaniya ya sanar a watan Janairu cewa zai bar ƙungiyar amma sai Laporta ya lallaɓa shi don ya ci gaba da zama a watan Afrilu.

Sai dai kuma ana ganin kalaman da Xavi ya yi na baya-bayan nan game da halin ƙarancin kuɗi a kulob ɗin ne suka ɓata wa Laporta rai.

Barcelona ta ce “ta gode wa Xavi bisa aikinda ya yi a matsayin koci” tun bayan da ya karɓi aikin a 2021.

Leave a Reply