Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Fursunoni Sun Yi Bore A Kaduna

Fursunoni sun yi bore a babban gidan yarin da ke birnin Kaduna a Arewacin Najeriya.

An ji karar harbe-harbe yayin da ‘yan gidan yarin ke yin bore, inji wasu rahotanni.

Fursunonin sun yi yunkurin afmfani da karfin tuwo su fita daga inda ake tsare da su, kafin jami’ai su dakile su, a cewar wasu shaidu.

Labarun Liberty ya ga an kawo karin ma’aikatan Hukumar Kula da Gidajen Yari, domin dakile masu boren.

An kuma girke sojoji da ‘yan sanda da jamia’n tsaron Civil Defence a ciki da wajen gidan yarin.

A hirarsa da Labarun Liberty, bayan kwantar da tarzomar, Mai Kula da Gidajen Yarin da ke jihohin Kaduna, Katsina, Jigawa da Kano, Muhammad Rabiu Babangida, ya ce matsalar ba ta taka ya karya ba.

Jami’in ya ce sun shawo kan matsalar, wacce ba bakuwa ba ce ga gidajen yari a fadin duniya kuma an riga an shawo kanta.

Muhammad Rabi’u kuma karyata labarun da ake yadawa cewa boren na da nasaba da rade-radin kawo masu cutar gidan yarin.

Ya kuma shawarci mazauna da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu domin tuni al’amura sun riga sun daidaita.

Exit mobile version