Home Home Filato: .’Yan Bindiga Sun Harbe Mutum Huɗu

Filato: .’Yan Bindiga Sun Harbe Mutum Huɗu

109
0

Mazauna ƙauyen Dong na Jihar Filato na cikin fargaba bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani wurin haƙar ma’adanai tare da kashe mutum huɗu.

Maharan sun kutsa wurin ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa ranar Asabar, inda suka harbe ma’aikatan.

Mai magana da yawun rundunar a Filato, Gabriel Ubah, ya ce sun tura ƙarin jami’an tsaro a yankin don dawo doka da oda.

Yan sanda na sane da abin da ya faru,” a cewarsa lokacin da aka tambaye shi game da faruwar lamarin.

Yan sanda sun je wurin da gaggawa. Sai dai abin baƙin ciki an kashe mutum huɗu da suka je wurin haƙar ma’adanan. An tsaurara tsaro a yankin.