Ministan matasa da habaka wasanni na Najeriya Sunday Dare ya taya tawagar kwallon kwando ta Najeriya ta mata murnar samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya.
D’Tigress sun doke abokan karawar su Mali a wasan share fage da suka yi a birnin Belgrade na Serbia da ci 73 da 69, wanda hakan ya basu damar samun tikitin zuwa gasar.
Kafin wasan tawagar D’Tigress ta doke Faransa wadda itace ta biyar a duniya da ci 67 da 65, bayan ta yi rashin nasara a hannun China.
Ministan wasannin ya jinjina wa ‘yan wasan, da ya ce Najeriya na alfahari da su.
A watan Satumba ne za a fara gasar ta FIBA 2022 a birnin Sydney na Australia.
Kafin zuwa gasar an samu rashin jituwa tsakanin ‘yan wasan da kuma hukumomin Najeriya, bayan da suka yi barazanar kin zuwa wasannin share fagen bisa kin biyan su kudin alawus din wasannin da suka yi a baya.
Sau uku D’Tigress na lashe kofin gasar kasashen Afrika, kuma su kadai ne daga nahiyar suka samu damar wakiltar Afrika.
You must log in to post a comment.