Home Coronavirus Fatawa: Babu Laifi Musulmai Su Yi Amfani Da Riga-Kafin Korona — Malaman...

Fatawa: Babu Laifi Musulmai Su Yi Amfani Da Riga-Kafin Korona — Malaman Dubai

279
0

Majalisar Fatawa ta Daular Larabawa wato UAE ta ce babu laifi ga Musulmai idan suka yi riga-kafin cutar korona ko da kuwa tana ɗauke da abin da addini ya haramta kamar sassan alade.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar na WAM ya ruwaito cewa malaman sun ce za a iya yiwa Musulmi allurar cutar ko da kuwa akwai abin haram matuƙar babu wani zaɓi.

Wannan fatawa tasu na zuwa ne yayin da wasu al’ummar Musulmi ke nuna shakku game da kayan haɗin allurar, wadda ake tunanin tana ƙunshe da ababen da Musulunci ya haramta ci ko shan su.

Riga-kafin korona na cikin abubuwan da aka sa su a matsayin kayan kariya ga ɗan Adam kamar yadda Musulunci ya tanada, musamman a lokutan annoba, inda mai lafiya ke shiga haɗarin kamuwa, wanda zai iya jawo haɗari ga al’umma baki ɗaya, a cewar majalisar.

A jiya Talata ne Dubai ta sanar cewa za ta fara yi wa ‘yan ƙasar riga-kafin korona a yau Laraba.