Home Labaru Fashi Da Makami: Gwamnatin Tarayya Ta Nuna Damuwa Kan Yankewa ‘Yan Najeriya...

Fashi Da Makami: Gwamnatin Tarayya Ta Nuna Damuwa Kan Yankewa ‘Yan Najeriya Hukuncin Kisa A Dubai

272
0

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin kasashen ketare Abike Dabiri Erewa, ta nuna takaici kan hukuncin kisa da aka yankewa wasu ‘yan Najeriya a hadaddiyar Daular Larabawa da aka samu da laifin fashi da makami.

Wannan na zuwa ne bayan kama wasu karin mutane 5 da suka yi fashi a cibiyar hada-hadar kudade a daular.

Dabiri, ta nuna damuwa kan yadda aka ci gaba da batawa Najeriya suna a idon duniya.

Bayan gudanar da bincike da shari’ar an tabbatar da cewa mutanen ne suka yi fashi a cibiyar tare da yin awon gaba da kudade da na’urar cire kudi.

Wasu da aka kaman sun amsa zargin da ake musu, yayin da wasu suka ki amsa zarge-zargen.

Rundunar ‘yan sandan Dubai sun tabbatar da cewa wadanda aka kaman sun bibiyi babbar motar dakon kudi, kafin daga bisani suka kai harin.

Leave a Reply