Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Fashewar Gas: Mutane Da Gidaje Da Motoci Sun Jikkata A Jibiya

1185392 Nigeria Tanker Explosion 92684

1185392 Nigeria Tanker Explosion 92684

Wata mummunar fashewar Gas ta da ta auku a Magama Jibia, garin da ke kan iyaka a Jihar Katsina, ta yi sanadiyyar mutane da dama sun jikkata, gidaje da motoci suka lalace.

Fashewar ta faru ne a wani gidan mai mai suna ‘Walidan’, kuma an danganta lamarin da fataucin gas daga Jamhuriyar Nijar.

Shehu Umar, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa wata motar dakon silindar gas da aka ajiye tsawon kwanaki a gidan man ne ya haddasa fashewar sakamakon wani tartsatsi daga wayar motar.

Wasu ganau sun tabbatar da cewa mutane da dama sun sami raunuka, yayin da gidaje, da motoci, da makarantu a kusa da wurin suka lalace, Mazauna yankin sun nuna damuwa kan fataucin gas ba tare da izini ba.

suna zargin cewa rashin kulawar hukumomi ya haifar da wannan musifa.

Mazauna yankin sun yi kira ga Gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakan gaggawa don hana irin wannan musifa faruwa a nan gaba, tare da kawo ƙarshen ayyukan fataucin gas a yankin.

Yanzu haka dai hukumomi suna kan tantance girman asarar da aka yi, amma har yanzu ba a fitar da wata sanarwa ba.

Exit mobile version