Home Labaru Fasakwauri: Mai Yiwuwa Nijeriya Ta Dage Haramcin Shigo Da Motoci

Fasakwauri: Mai Yiwuwa Nijeriya Ta Dage Haramcin Shigo Da Motoci

786
0

Shugaban hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya Kanar Hameed Ali mai ritaya, ya ce mai yiwuwa Nijeriya ta dage haramcin shigo da motoci ta iyakokin ta na tudu.

Kanar Hamid Ali, ya ce dage haramcin shigo da motoci daga Cotonou zai tabbata ne, idan hukumar tare da takwarar ta ta kasar Benin sun yi nasarar aiwatar da shirin fasahar kimiyya ta zamani, wadda za ta rika tattara bayanan duk kayan da za a rika safarar su a kan iyakokin kasashen biyu.

Yayin da ya ke karin bayani a kan halin da ake ciki, shugaban jami’in shashen yada labarai da fasahar sadarwa na hukumar Benjamin Aber, ya ce da zarar sabon shirin hadin gwiwar ya soma aiki, za a janye dukkan shingayen bincike da jami’an kwastam su ka kafa a yankunan da ke da kusanci da iyakoki da sauran wuraren da su ka saba tsayuwa.

Idan dai ba a manta ba, a cikin watan Janairu na shekara ta  2017 ne, gwamnatin Nijeriya ta haramta shigo da motoci ta kan iyakokin ta na tudu daga makwafciyar ta Jamhuriyar Benin, domin magance matsalar fasakwaurin motocin da ake yi ba tare da biyan haraji ba.

Leave a Reply