Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Jihohin Bauchi da Gombe, a fafautukar neman goyon bayan wakilai a zaben fidda gwani na takarar neman wanda jam’iyar APC za ta tsaida takarar Shugaban kasa.
Ma manufar ziyar Osinbajo dai ita ce ganawa da ‘yan siyasa, ya amma ya kan kai ziyarar girmamawa ga Iyayen kasa da kuma ziyartarn manyan malaman Addini.
A fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, Farfesa Yemi Osinbanjo ya bayyana farin ciki dangane da ci-gaban da ya gani a jihar Bauchi, ya kuma mika gaisuwar shugaba Buhari ta musamman ga Sarkin Bauchi, inda ya ce sama da shekaru bakwai kenan ya ke mataimakin shugaban kasa, sannan ya bada tabbacin cewa ya samu gogewa kwarai a kan tafiyar da harkar gwamnati.
Mai martaba Sarkin Bauchi Rilwan Sulaiman Adamu, ya bayyana farin cikin sa da na al’ummar masarautar bisa ziyarar da Osinbajo ya kai, inda ya ce hakan ya nuna irin muhimmanci da darajar da mataimakin shugaban kasar ke nuna wa masarautu.