Home Labaru Farfado Da Lantarki: Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 600

Farfado Da Lantarki: Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 600

559
0

Kamfanin da ke kula da yadda ake rabar da wutar lantaki na kasa TCN ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya ta amince da zuba naira biliyan 600 cikin kasuwar wutar lantarkin kasar nan.

Injiniya, jami’in gudanarwa na kamfanin  Edmund Ejie ne ya sanar da hakan  a ranar Larabar data gabata. A cewar sa, a lokacin wata ganawa da yan jarida bayan kammala wata ganawa da masu ruwa da tsaki na ma’aikatar a babbar birnin tarayya, Abuja.

Ya ci gaba da  cewa, za a fara rabon kudin ne a kowani lokaci daga yanzu. Ya kara da cewa,  wannan yunkuri na biyan ragin da aka samu ne ta bangaren biyan kudin wutar lantarki a kasuwanni baki daya.

Jami’in ya kuma yi nuni da cewa,   wannan yunkuri da gwamnatin tarayya tayi na kasuwar ne baki daya, ba wai na wani bangare guda ba.

A wata sabuwa kuwa,a rahoto a baya cewa, kamfanonin da ke rarraba wutar lantarki na Nijeriya wato NEPA (DISCOs) ta nuna shakku akan shirin Gwamnatin Tarayya na biyan naira biliyan 736 ga manyan yan kasuwa domin sake mallakar kamfanonin wutar lantarki.

Rahotannin baya-bayan nan dai sun bayyana cewa Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sake kwato kamfanin rarraba wutar lantarkin na kasar nan daga hannun yan kasuwa don ceto kasar nan daga cikin matsalar da ta jima tana fuskanta na wutar.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an tursasa 17 daga cikin tashoshin samar da wutar lantarki 27 a fadin kasar tsayar da ayyuka a wasu daga cikin ma’aikatunsu sakamakon karancin bukata daga DISCO da kuma tabarbarewar samar da wutar lantarki ga miliyyoyin abokan hulda.

Leave a Reply