Home Labaru Farawa Da Iyawa: Sanatocin APC Sun Ki Yarda A Yi Muhawara A...

Farawa Da Iyawa: Sanatocin APC Sun Ki Yarda A Yi Muhawara A Kan Jawabin Buhari

455
0
Sanata Istifanus Dung Gyang

Sanatocin jam’iyyar APC, sun dakile batun da ke neman majalisar dattawa ta yi muhawara a kan Jawabin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a wajen bikin ranar Damokradiyyar Nijeriya.

Sanata Istifanus Dung Gyang na jam’iyyar PDP ne ya gabatar da batun a zauren majalisar dattawa, inda ya bukaci abokan aikin sa su amince a tattauana batun a matsayin abu mai muhimmanci a Nijeriya.

 Ya ce batun ya na da alaka da jawabin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a ranar Dimokardiyya, wanda ya yadu ya kuma janyo ce-ce-ku-ce da dama.  

Yayin da shugaban majalisar Ahmed Lawan ya ba ‘yan majalisar damar neman matsaya a kan lamarin, yawancin sanatocin, wadanda akasarin su ‘yan jam’iyyar APC ne sun ki amincewa da hakan.