
A karon farko cikin shekaru 17, tsadar farashin kayayyakin masarufi ta karu da kashi 20 da rabi 5 cikin 100 a Najeriya cikin watan Agusta da ya gabata.
Rabon da a ga irin wannan tashin gwauron-zabon dai tun watan Satumba na shekara ta 2005.
Alkaluman da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar sun nuna cewa, adadin ya karu ne daga sama da kashi 19 da aka gani a cikin watan Yuli.
Lamarin dai ya haifar da tada jijiyoyin wuya a Nijeriya, wadda ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, yayin da babban bankin CBN ya shiga cikin matsin lambar kara kudaden ruwa.
Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke ci- gaba da kokawa game da halin matsin rayuwa sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan.
You must log in to post a comment.