Home Labaru Kasuwanci Farashin Kayan Abinci: Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Sa Ido A 2021

Farashin Kayan Abinci: Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Sa Ido A 2021

566
0
Gargadi: Shugaba Buhari Ya Yi Magana A Kan Rikicin Shugabancin APC

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Sha Alawashin sa ido yadda ya kamata domin tabbatar da cewa ba a sami hauhawar farashin kayan abinci a sabuwar shekarar 2021 ba.

Shugaban ya yi alkawarin ne yayin taron Majalisar Ba da Shawara kan Harkokin Tattalin Arziki karo na biyar wanda ya gudana a Fadar Shugaban Kasa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa duk da bude wasu iyakokin kasar nan da aka yi, har yanzu ba’a bada damar shigo da shinkafa da kuma kaji ba.

Shugaban ya kuma umarci Babban Bankin Kasa (CBN) da kada ya kuskura ya ba masu shigo da abinci canjin kudaden kasar waje.

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Ministar Kudi, Zainab Ahmed da ministan Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar-Farouk.

Leave a Reply