Karo na uku kenan a jere da sama da mutane dubu 7 ke kamuwa da cutar ta coronavirus a Faransar daga Juma’ar da ta gabata zuwa yau lahadi.
Kawo yanzu dai jumillar mutane dubu 30 da 698 annobar ta kashe a Faransa.
Ranar lahadin ce dai hukumomin Faransar suka sanya karin yankunan kasar 7 cikin jerin wadanda suke da hadarin gaske sakamakon sake barkewar da annobar coronavirus ta yi karo na biyu a yankunan.
Karin sassan da hukumomin Faransar suka bayyana cikin masu hadarin yaduwar annobar at coronavirus sun hada da Lille, Strasbourg da kuma Dijon.
A halin yanzu hukumomin lafiya sunce yawan mutanen da annobar coronavirus ta halaka ya kai akalla dubu 880 da 396, daga cikin mutanen miliyan 26 da dubu 947 da 550 da suka kamu da cutar a sassan duniya.
Sai dai daga cikin jumilar adadin akalla mutane miliyan 17, da 709 da 800 sun warke.