Home Labaru Faransa: Limaman Katolika Sun Lalata Kananan Yara Dubu 216

Faransa: Limaman Katolika Sun Lalata Kananan Yara Dubu 216

177
0

Shugaban darikar Katolika na Duniya Fafaroma Francis ya bayyana matukar kaduwa da rahoton da ke bankado yadda kananan yara fiye da dubu 200 suka fuskancin cin zarafi ta hanyar lalata a majami’ar Katolika da ke Faransa.


Sakamakon binciken wanda ya bankado yadda limaman Majami’ar Katolika a Faransa suka lalata kananan yara dubu 216 daga shekarar 1950 zuwa 2020, sakamakon da ke matsayin tonon sililin da aka shafe shekaru ana rufa-rufa akansa.
Binciken wanda wata hukumar kare hakkin kanana yara mai zaman kanta a Faransar ta shafe shekaru 2 da rabi tana yi, ya bayyana damuwa da samun makamantan cin zarafin wanda ke matsayin kari kan wanda aka rika gani cikin shekarun nan a wasu kasashe na Turai.


Acewar Shugaban darikar ta Katlika Fafaroma Francis rahoton abin damuwa ne matuka, ko da ya ke akwai bukatar jinjinawa wadanda abin ya shafa da suka cire tsoro ta hanyar sanar da abin da ya faru da su.


Shugaban hukumar da ta jagoranci binciken, Jean-Marc Sauve ta ce alkaluman yaran da suka fuskanci cin zarafi daga malaman makarantun da ke karkashin cocin ta Katolika da kuma limam majami’ar ya kai kololuwa zuwa yara dubu 330 cikin shekaru 7 a sassan Duniya.

Leave a Reply