Home Labaru Fara Aikin Sabbin Ministoci: Fadar Shugban Kasa Ta Soke Zaman FEC Na...

Fara Aikin Sabbin Ministoci: Fadar Shugban Kasa Ta Soke Zaman FEC Na Wannan Makon

309
0

Fadar shugaban kasa ta ce ba za a yi zaman majalisar zartar wa da aka saba yi kowanne mako ba a ranar Laraban nan 4 ga watan Satumba.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata, ta ce an soke taron na wannan makon ne saboda a ba ma’aikatu damar duba takardun su da majalisar zartarwa ta kammala nazari ta kuma mayar musu.

mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu

Sanarwar har ila yau tace dage taron zai ba sabbin ministoci damar cigaba da tattauna wa da manyan jami’an ma’aikatun su domin sanin makamar aiki.

Hakazalika za su yi amfani da lokacin wajen shiryawa tare tsara kasafin kudin ma’aikatun su na shekarar 2020.