Home Labarai Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Maganar Dan Takarar Buhari

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Maganar Dan Takarar Buhari

50
0

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da zargin da ake yi cewa akwai wasu boyayyun mutane da ke juya madafun iko a fadar.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya karyata rade-radi ne bayan zaben jam’iyyar APC a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Garba Shehu ya fitar da sanarwar ne domin bayyana irin rawar da shugaba Buhari ya taka a zaben fidda dan takarar jam’iyyar APC.

Ya ce wasu mutane su na tunanin idan mutum shugaba ne, shi kenan zai mamaye komai har ya kutsa kai cikin sakamakon zabe.