Fadar shugaban kasa ta maida martani a kan hasashen da ake
ta yi cewa an kammala tattara sunayen ministocin Shugaba
Bola Ahmed Tinubu.
Mai magana da yawun shugaban kasa Dele Alake bayyana haka yayin da ya ke maida martini a kan has ashen, inda ya ce ba a tattara jerin sunayen mistocin ba.
Dele Alake, ya ce babu alamar gaskiya a jita-jitar da ake yadawa game da jerin mistocin shugaba Tinubu.
Ya ce idan Shugaba Tinubu ya shirya kuma ya natsu, ‘yan jarida ne farkon wadanda za su san abin da ake ciki.

