Home Labaru Ilimi EU Ta Tallafa Wa INEC Da Kayan Aiki Don Inganta Harkokin Zaɓe...

EU Ta Tallafa Wa INEC Da Kayan Aiki Don Inganta Harkokin Zaɓe A Nijeriya

1
0

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta samu
kyautar wasu kayan aiki daga ƙungiyarTarayyar Turai EU,
wadada za su taimaka wajen inganta harkokin zaɓe a Nijeriya.

Shugabanb hukumar zaɓe Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka lokacin karɓar kayayyakin a Abuja, inda ya ce kayan aikin za su taimaki hukumar zaɓe wajen inganta harkokin zaɓen ta.

Farfesa Mahmood Yakubu ya ƙara da cewa, akwai wasu ƙarin kayayakin masu yawa da ƙungiyar EU za ta ba hukumar.

Kungiyar Tarayyar Turai dai na daga cikin kungiyoyin da ke sa ido a kan zaɓubbukan Nijeriya, inda a lokuta da dama ta ke cewa ana tafka kura-kurai a tsarin zaɓen Nijeriya.