Home Home El-Rufai Ya Jinjina Wa Sojoji Kan Kashe Kasurgumin Dan Bindiga, Danwasa A...

El-Rufai Ya Jinjina Wa Sojoji Kan Kashe Kasurgumin Dan Bindiga, Danwasa A Kaduna

77
0
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya yaba wa dakarun sojin Operation Forest Sanity bisa nasarar da su ka samu ta hallaka kasurgumin dan bindiga Isiya Danwasa a karamar hukumar Igabi.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya yaba wa dakarun sojin Operation Forest Sanity bisa nasarar da su ka samu ta hallaka kasurgumin dan bindiga Isiya Danwasa a karamar hukumar Igabi.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar.

Danwasa dais hi ne musabbabin kashe-kashen jama’a da yin garkuwa da mutane da kuma satar shanu a wasu yankunan jihar Kaduna.

Dakarun sojin, sun samu nasarar kashe dan bindigar ne yayin wani kwanton-bauna da su ka yi a yankin Sabon Birni da ke karamar hukumar Igabi. Gwamna El-Rufa’i, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kaduna su cigaba da ba jami’an tsaro sahihan bayanai domin ci-gaba da magance kalubalen rashin tsaro a fadin jihar.