Mai ba Jam’iyyar APC Shawara a Kan Harkokin Shari’a, Ahmed El-Marzuk, ya yi murabus daga kwamitin zartarwa na jam’iyyar na ƙasa.
Rahotanni sun ce, El-Marzuk ya yi murabus ne sakamakon dagewar da wasu abokan aikin sa suka yi na cewa ba zai iya cigaba da zama a kan aiki ba saboda wasu zarge-zarge da ake yi masa.
Wata Sanarwa da ya fitar, El-Marzuk ya ce bisa abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar APC, ya ga ya dace ya ajiye muƙamin sa domin bada damar sake fasalin shugabancin jam’iyyar.
El-Marzuq ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran jami’an jam’iyyar saboda damar da su k aba shi ta yi wa jam’iyyar hidima.