Hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta Najeriya ta gargadi masu tukin direbobi su gujewa tukin ganganci gabannin bikin babbar Sallah.
Karanta Wannan: An Fara Yi Wa Jami’an Tsaron Nijeriya Binciken Kwakwalwa
Kwamandan hukumar na jihar Oyo, Cecilia Alao, ta yi gargadin a lokacin da take Magana da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, inda ta bukaci masu mota a su bi ka’idoji a lokacin Sallah da bayan Sallah.
Ta ce mafi akasarin jami’an hukumar ba za su yi bikin babban Sallah ba, domin za a tura su wurare daban-daban domin tabattar da tsare masu amfani da hanyoyi.
Ta ce aikin su shi ne tabbatar da tsaron al’umma da za su bi hanyoyi da kuma tabbatar da ganin, an yi aiki yadda ya kamata, saboda haka ne aka gudanar da taron wayarwa jama’a kai akan ilimin tuki gabannin bikin babban Sallah.
Cecilia
Alao ta kara da cewar idan har masu ababen hawa za su bi ka’idar tuki, mai yiwuwa ayi bikin Sallah, ba tare da hatsari ba.