Home Labaru EFFC Ta Bukaci Kotu Ta Hana Maina Beli

EFFC Ta Bukaci Kotu Ta Hana Maina Beli

559
0
Abdulrasheed Maina, Tsohon Shugaban Hukumar Fansho
Abdulrasheed Maina, Tsohon Shugaban Hukumar Fansho

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce AbdulRashind Maina ba mutumin kirki ba ne kuma ba ya ganin girman dokar Nijeriya.

EFCC ta ce, idan har aka ba shi beli, tabbas gudu zai yi daga Nijeriya, ta na mai jaddada cewa Maina ya yi rub-da-ciki da kudi naira Biliyan 3 na ‘yan fansho ba tare da wani boye-boye ba.

Hukumar EFCC ta cigaba da cewa, Maina ya na da takardar zama dan kasar Amurka, kuma mazaunin kasar Dubai ne, kuma duk da cewa wa’adin fasgon shin a shiga kasa da kasa yak are, amma, ya na fita daga Nijeriya ta iyakokin Sokoto da Katsina masu makwaftaka da kasar Nijar.

EFCC ta bukaci Alkalin kada ya ba AbdulRashid Maina beli, saboda sai da aka sha bakar wahala kafin a kama shi bayan shekaru 7 ana neman shi ruwa a jallo.

Leave a Reply