(EFCC) ta ƙi amincewa da buƙatar tsohon Gwamnan babban Bankin Nijeriya, Emefiele na a sake masa fasfo ɗinsa na tafiya ƙasar waje.
Lauyan da ke kare Emefiele dai ya shigar da takardar shaida yana neman a ba shi fasfo din domin a ba shi damar zuwa ƙasar Ingila domin jinya,
Lauyan masu gabatar da ƙara Muhammad Abbas Omeiza ya bayyana cewa babu wani rahoton likita da aka gabatar wa kotu
da ke tabbatar da rashin lafiyar Emefiele da ke buƙatar jinya a ƙasashen waje.
Ya ƙara da cewa, duk wata matsala ta rashin lafiya za a iya magance ta a Nijeriya,
yana mai jaddada cewa Emefiele ya ajiye fasfo ɗinsa a gaban kotu a matsayin wani ɓangare na sharuɗɗan belinsa,
wanda bai kamata a riƙa maganar karɓarsa ba.
Omeiza, ya ƙara nuna damuwa game da yiwuwar Emefiele na iya gudawa idan ya samu jirgin sama,
domin yana da alaƙa da ƙasashen duniya da zai iya haɗa baki da wasu a ƙasashen waje ya tsere