Home Home EFCC Ta Gayyaci Sirika Don Amsa Tambayoyi Kan Dodoridon Jirgin Nijeriya

EFCC Ta Gayyaci Sirika Don Amsa Tambayoyi Kan Dodoridon Jirgin Nijeriya

92
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika domin bincike a kan aikin samar da Jirgin Nijeriya a karkashin kamfanin ‘Nigeria Air’.

Hadi Sirika dai zai iya bayyana a gaban hukumar a cikin makon nan, domin amsa tambayoyi a kan kaddamar da Jirgin Nijeriya da kuma zargin kashe naira biliyan 3 a kan shirin samar da Jirgin Nijeriya.

Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya tabbatar da cewa, akwai binciken da su ke ci-gaba da yi a kan zargin da ke makale ga aikin samar da Jirgin Nijeriya, amma bai bada cikakken bayani a kan hakan ba.

Wasu majiyoyi daga hukumar EFCC sun ce, hukumar za ta binciki naira biliyan uku da aka ce sun bace ne da sunan aikin.

Tunin dai hukumar EFCC ta gudanar da tambayoyi a kan wasu jami’an kamfanin Nigerian Air game da kaddamar da Jirgin Nijeriya da aka yi kwanakin baya a Abuja.

Leave a Reply