Hukumar yaki da cin hanci da ashawa EFCC, ta cika takardun kotu domin kwace wasu kadarori da aka gano su na da nasaba da tsohon Shugaban hukumar fansho ta Nijeriya Abdulrasheed Maina.
EFCC, ta kuma cika wata takarda domin samun umurnin tsare Abdurrasheed Maina, wanda a makon da ya gabata ne jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS su ka mika mata shi bayan sun kama shi a wani Otal da ke Abuja.
Baya ga gidaje, EFCC ta gano wasu kamfanoni biyar, wadanda ta ce Maina ya na amfani da su wajen hamdame kudi, sannan ta bukaci ya samar da cikakken bayanin kudi da ke asusun kamfanonin.
Jerin kamfanonin dai ya hada Cluster Logistics, da Drew Investment & Construction Ltd, da Kongolo Dynamics Cleaning Ltd, da Dr Abdullahi A. Faizal, da Nafisatu Aliyu Yeldu da kuma Abdulrasheed Abdullahi Maina.
Alamu na nuni da cewa, za a gurfanar da Maina a gaban kotu cikin wannan makon, domin amsa tuhume-tuhumen hukumar EFCC da Gwamnatin tarayya da ke kan sa.