Home Home EFCC Da CCB Sun Gayyaci Muhyi Magaji Rimin Gado

EFCC Da CCB Sun Gayyaci Muhyi Magaji Rimin Gado

1
0

Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa EFCC, da hukumar kula da da’ar ma’aikata sun gayyaci shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhuyi Rimingado domin amsa tambayoyi a kan kudaden hukumar.

Idan dai ba a manta ba, a baya dai Rimingado ya ce ya gudanar da bincike a kan faifan bidiyon da ke nuna tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya na karbar wasu makudan daloli da ake kyautata zaton cin hanci ne.

Gwamna Ganduje dai ya samu umarnin wucin gadi da ya hana hukumar gudanar da bincike a kan sa da iyalan sa da kuma duk wani mai rike da mukaman siyasa a lokacin mulkin sa.

Sai dai a wani abin da ake ganin ana takun saka da Gwamna Ganduje, a lokaci guda hukumomin EFCC da CCB sun kaddamar da bincike kan ayyukan Rimingado a hukumar.

A cikin wata Wasika, EFCC ta ce ta na binciken wani lamari da bukatar samun wasu bayanai daga ofishin Rimingado wanda ya zama wajibi, yayin da hukumar CCB ke neman Rimingado ya bayyana bayanan wasu kudade da hukumar shi ta kwato daga shekara ta 2016 zuwa yau.