Kungiyar Tattalin Arzikin ƙasashen Afirka ta yamma
ECOWAS, ta yi Allah-Wadai da garkuwa da yara 80 da aka yi
a yankin arewacin Nijeriya cikin makon da ya gabata.
Mafi yawan waɗanda aka yi garkuwa da su a jihar zamfara dai mata ne da kananan yaran da su ka je sharar gona da yin itace a daji.
A cikin wata sanarwa da ECOWAS ta fitar, ta yi kira da a saki yaran, sai dai har yanzu babu wanda ya ɗauki alhakin sace kananan yaran.
Harin dai shi ne na baya-bayan nan a jihar Zamfara, wadda ke fama da yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.
You must log in to post a comment.