Home Labaru Duniya Labari: Al-Makura Ya Mika Wa Sabon Gwamna Makullan Gidan Gwamnati

Duniya Labari: Al-Makura Ya Mika Wa Sabon Gwamna Makullan Gidan Gwamnati

584
0

Gwamnan jihar Nasarawa mai barin gado Umaru Tanko Al-Makura, ya mika makullan gidan gwamnati da ke Lafia ga gwamna mai jiran gado Injiniya Abdullahi Sule.

Almakura dai ya mika makullan ne, yayin wani taro da ya samu halartar ma’aikatan gidan gwamnati bayan iyalan sa sun bar gidan kafin a fara.

Gwamna Al-Makura, ya ce sun shafe sa’o’i suna ganawa da wanda zai maye gurbin sa, ya na mai cewa a shirye ya ke ya bada bayanai a kan ayyukan da aka kaddamar da yadda aka gudanar da mulki a shekarun da su ka gabata.

A na shi bangaren, gwamna mai jiran gado Injiniya Abdullahi Sule, ya ce su na shaidar Al-Makura na daya daga cikin natsatsun mutanen da su ka yi shugabanci mai inganci.

A karshe ya yi wa al’ummar jihar Nasarawa alkawarin inganta jihar fiye da yadda ya same ta, tare da yi wa Al-Makura da iyalan sa addu’ar samun kariyar Allah.

Leave a Reply