Zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bar Nijeriya
da zuwa kasar Turai.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Tunde Rahman ya fitar, ya ce Tinubu ya kai ziyarar aiki kuma ya na shirin tattaunawa da masu zuba jari da sauran manyan abokan huldar sa domin daidaita shirin mika mulki tare da wasu manyan mukarraban sa.
Sanarwar dai ba ta bayyana ainihin inda Tinubu nufa a nahiyar Turai ba, amma ta ce zai dawo nan ba da dadewa ba domin shirye-shiryen rantsar da shi a hukumance a matsayin shugaban kasa.
Idan dai baa manta ba, za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin sh8ugaban Nijeri ne a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2023.