Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya fusata, lokacin da ya
ke bibiyar yadda aka raba wa manoma tallafin korana a
karamar Hukumar Rimgin.
Umar Namadi daoi ya kai ziyara ne domin gano yadda talakawa manoma su ka amfana ko akasin haka da kudin tallafin Korona da Bankin Duniya ya ba Jihar ta Jigawa kyauta, domin rage raɗaɗin talauci samakon kullen Korona.
Manoma a fadin Jihar ta Jigawa dai sun amfana da kyautar taki da maganin feshi daga tallafin na Bankin Duniya, wanda gwamnan ya ke zargin ba a ba manoman ba kamar yadda aka tsara.
Umar Namadi, ya yi rantsuwa cewa duk wanda ya ci kudin tallafin sai ya biya.