Home Labaru Kiwon Lafiya Duk Minti Daya Cutar Kanjamau Na Kashe Mutum Daya A Duniya

Duk Minti Daya Cutar Kanjamau Na Kashe Mutum Daya A Duniya

218
0

Wani sabon rahoto na hukumar yaki da cutar kamjamau ta Majalisar Dinkin Duniya, UNAIDS, ya nuna cewa cutuka da ke da nasaba da Aids sun rika kashe mutum daya a duk minti daya a shekarar 2021.

Haka kuma rahoton ya yi kiyasin cewa a duk minti biyu a shekarar ta 2021 budurwa daya ko matashi na kamuwa da kwayar cutar mai karya garkuwar jiki, HIV.

Rahoton wanda aka fitar a babban taron hukumar a Montreal, Canada, ya nuna cewa a fadin duniya manyan mata da ‘yan mata su ne kashi 49 cikin dari na sabbin masu kamuwa da cutar a 2021.

Amma kuma a yankin kudu da hamadar Sahara matan da ‘yan mata su ne kashi 63 cikin dari na sabbin masu kamuwar a wannan shekara.

Alkaluman sun nuna cewa akalla mutum miliyan daya da rabi ne sabbin wadanda suka kamu da kwayar cutar ta HIV.

Kazalika rahoton ya yi nuni da cewa ana samun karuwar sabbin masu kamuwa da cutar a wuraren da a da ake samun raguwa.

Duk da haka shugabar hukumar Winnie Byanyima ta ce idan aka tashi tsaye za a iya kawo karshen cutar ta Aids zuwa shekara ta 2030. rahoton ba ya yana nufin

Leave a Reply