Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Duk Mai Son Mulkin Nijeriya Dole Ya Yi Yarjejeniya Da Arewa – Bakare

Babban malamin coci a Nijeriya Fasto Tunde Bakare, ya ce duk mai son ya mulki Nijeriya sai ya yi yarjejeniya da yankin arewa.

Yayin zantawar sa da manema labarai, Fasto Bakare ya ce arewa ta na da hanyar maida mutum shugaban je ka na yi ka.

Tunde Bakare, ya ce za a iya sauya hakan ne kawai ta hanyar sauya kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Ya ce tsarin da kundin tsarin  mulkin ya ke a kai yanzu, duk wanda zai mulki Nijeriya sai ya yi yarjejeniya da yankin arewa, domin ita ke da hanyar dora mutum a kan mulki.

Faston ya kara da cewa, duk abubuwan da arewa ke da su a lokacin su Ahmadu Bello a yanzu babu su, domin duk masana’antun da arewa ke da su sun zama tarihi, sannan babu dalar gyada da sauran su, abin da kawai ‘yan arewa ke da shi a yanzu shi ne mulki da karfin iko.

Tunde Bakare ya ƙara da cewa, Nijeriya ƙasa ce da babu bangaren da zai iya cin zabe da kan sa, domin dan kudu ba zai iya cin zabe ba tare da neman ‘yan arewa ba.

Exit mobile version