Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya komo gida Najeriya bayan bulaguron da ya yi domin duba lafiyar sa a Birtaniya.
A wani saƙo da mai taimakawa shugaban na musamman kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya wallafa a shafin sa na Tuwita da maraicen ranar Lahadi, ya ce shugaba Buhari, ya sauka a birnin Abuja.
Shugaban kasan dai ya kwashe kusan mako biyu ne a birnin Landan, bayan da ya bar Najeriya a ranar 31 ga watan Oktoba domin a duba lafiyar sa Landan.
A lokacin bulaguron na sa Shugaban Buhari, ya ziyarci sarki Charles lll a fadar sa da ke Buckingham.
You must log in to post a comment.