Home Home DSS Ta Fara Cafke Wasu Kan Zargin Karkatar Da Tallafin Rage Radadi...

DSS Ta Fara Cafke Wasu Kan Zargin Karkatar Da Tallafin Rage Radadi Na Jihohi

2
0

Huhumar Tsaron Farin Kaya DSS ta kama wasu da take zargi da hannu a karkatar da tallafin rage radadi da aka samar domin tallfawa al’umma.

DSS ta ce ta dauki matakin ne bayan samun rahotonni daga gwamnatocin wasu jihohi dangane da batun da ke da alaka da sama da fadi ko sayar da kayayyakin tallafin da aka samar domin taimakon al’umma.

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ne ya shaida hakan a wata sanarwar da ya fitar.

Ya ce bayan bincike da aka yi, an kama wasu da ake zargi da aikata laifuka a jihar Nasarawa da ke da hannu wajen karkatar da kayayyakin abinci da aka tanadar wa marasa galihu a jihar.

Afunanya ya kara da cewa hakan ya sa suka gudanar da bincike kan batun kuma kawo yanzu sun kwato wasu kayayyakin.