Home Home DSS Ta Cafke Tsohon Soja Da Lauya Da Wasu Kan Zargin Ta’addanci

DSS Ta Cafke Tsohon Soja Da Lauya Da Wasu Kan Zargin Ta’addanci

11
0

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta ce ta gudanar da wani samame tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro a jihar Kogi, inda rundunar ta kama wasu gungun masu aikata laifuffuka su shida a Gegu Beki da ke Lokoja a kan hanyar Abuja.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ya fitar, ya ce mutanen da aka kama sun hada da wani kanar AU Suleiman mai ritaya, da Barista MK Aminu, da Kabir Abdullahi da Isah Umar da Kadir Echi da Adama Abdulkarim.

Makaman da aka kwato daga hannun mutanen sun hada da bindiga kirar gida, da ta AK47 da wasu jimillar kudi.

Haka kuma, jami’an tsaron sun kama wani matashi da ake zargi da yin garkuwa da mutane mai suna Haruna Adamu a kauyen Fotta da ke karamar hukumar Gombi ta jihar Adamawa.