Home Labaru Doke Argentina: Saudiya Ta Bada Hutu a Daukacin Kasar

Doke Argentina: Saudiya Ta Bada Hutu a Daukacin Kasar

125
0

Sarki Salman na Saudiya ya bada umarnin hutu a yau Laraba ga daukacin ma’aikatan kasar baki daya sakamakon nasarar da kasar ta samu ta doke Argetina da kwallaye 2-1 a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.

Kazalika hutun ya shafi daukacin daliban makarantu da kamfanoni masu zaman kan su duk dai don nuna murnar doke Argentina wadda ke cikin bakin-cikin kashin da ta sha.

Yarima Mai Jiran Gadon Saudiya, Mohammed bin Salman, shi ne ya bada shawarar bada hutun-gama garin.

Tawagar kwallon kafa ta Saudiya da ake kira Green Falcons ta kunyata gwarzon dan wasan duniya, wato Lionel Messi a wasan wanda ya gaza ceto kasar sa daga hannun Saudiya.

Argentina ce ta fara zuwa kwallo ta hannun Messi a bugun fanariti a minti  na 10 da saka wasan, amma Saudiya ta farke ta hannun Saleh Al-Shehri a minti na 48, kafin  Salem Al Dawsari ya kara ta biyu a minti na 53.

Tuni manazarta suka bayyana wannan nasarar ta Saudiya a matsayin wani gagarumin al’amari da ya girgiza duniyar tamola.

Leave a Reply