Home Labaru Dokar Kasa: Shugaba Buhari Da Osinbajo Sun Bayyana Kadarorin Su

Dokar Kasa: Shugaba Buhari Da Osinbajo Sun Bayyana Kadarorin Su

523
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi tsarin dokar kasa, inda ya mika wa hukumar kula da da’ar ma’aikata takardar da ta nemi ya cike domin bayyana kadarorin da ya mallaka gabanin sake rantsar da shi a wa’adin mulki na biyu.

Dokar Nijeriya dai ta jaddada cewa, dole shugaban kasa da mataimakin sa sai sun bayyana kadarorin su kafin a rantsar da su.

A ranar Larabar nan ne aka sake rantsar da shugaba Buhari da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a wa’adin na biyu.

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa an dan samu canji a yawan kadarorin da shugaba Buhari ya bayyana ya mallaka a 2015, amma ba wani mai yawa ba.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya cika takardar, kuma tun ranar Talatar da ta gabata aka maida wa shugaban Hukumar kula da da’ar ma’aikata Mohammed Isa.

Garba Shehu, ya ce babu karin yawan gidaje, babu asusun ajiyar kudade a bankunan ciki da wajen Nijeriya, kuma babu karin hannayen jari.

Leave a Reply