Jam’iyyar PDP ta ce sabon umarnin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar akan janye tallafi akan shigo da kayan abinci bai dace ba.
Jam’iyyar ta ce idan aka yi la’akari da halin kuncin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki, bai kamata shugaban kasa ya yanke wannan shawarar ba.
A wannan makon ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ba babban bankin Najeriya CBN umarnin ya daina bayar da tallafin sauyin kudi ga masu kasuwancin shigo da abinci cikin Najeriya.
Mai Magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya ce shugaban kasa ya bayar da wannan umarni ne domin inganta cinikin kayan abincin da aka noma a cikin gida.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta yi amfani da kudin tallafawa masu shigo da kayan abinci wajen inganta tattalin arziki. Sakataren yada labarai naJam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan, ya ce sabon umarnin zai kawo lalacewar ingancin abincin da jama’a za su ke ci, sannan kuma ya kara jefa kasa cikin halin tsanani, bayan wanda ake fama da shi a yanzun.