Home Labaru Doka: Gwamnatin Kano Ta Haramta Taron Gangamin Jama’a

Doka: Gwamnatin Kano Ta Haramta Taron Gangamin Jama’a

353
0

Wata sanarwa da maimagana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya fitar ta ce an haramta zanga-zanga da duk wani taro da ya shafi gangamin jama’a a fadin jihar har sai baba ta gani.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an dauki matakin ne don kaucewa duk wata barazana ga zaman lafiya da kuma karya doka baya ga matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Sanarwar ta yi gargadi ga jama’ar jihar da kungiyoyin farar hula su mutunta dokar wacce ba a fadi lokacin dage ta ba, domin duk wanda aka kama da laifin saba dokar za kama shi kuma a hukunta shi.

Leave a Reply