Home Labaru Doka: Gwamnatin Jigawa Ta Soke Bukukuwan Babbar Sallar

Doka: Gwamnatin Jigawa Ta Soke Bukukuwan Babbar Sallar

423
0

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar ya soke bukukuwan babbar Sallar a jihar da kuma dakatar da sarakuna biyar masu daraja na jihar daga jagorantar duk wani hawan Sallah da kuma hawan daushe a wannan shekarar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin  zantawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

Abubakar ya ce, wannan umurnin na daga cikin yunkurin gwamnatin jihar na ci gaba da yaki domin dakile yaduwar cutar COVID-19.

Ya bayyana cewa, jihar ta samu gagarumar nasara ta wannan fuskar, kasancewar bata samu bullar cutar ba kusan kwanaki 30 da suka gabata.

To sai dai Gwamnan yace duk da irin wannan nasarar, dole ne jihar ta bi duk wasu matakai na dakile bullar cutar da kuma daukar matakan kariya na dakile yaduwarta. Ya ce kawo yanzu mutum daya ne kawai ya rage a cibiyar killace masu dauke da cutar covid-19, yayinda aka rufe cibiyon kula da masu fama da cutar dake Fanisau da Birninkudu.

Leave a Reply