Akalla matasa 150 ne suka fara samun Horo na makwanni kan yadda ake shuka itatuwa da fulawa da kuma kiyon kifi da sauran ayyukan gona a Kadana.
Matasan za su sami horon ne a makarantar horar da ayyukan gona ta Teku Farm dake Mahuwa a yankin karamar hukumar Igabi da ke Kaduna.
Shugaban Teku farm Alhaji Ibrahim Salisu, ya bayyana haka a lokacin da yake magana da manema labarai jim kadan bayan an fara horar da matasan.
Ibrahim Salisu, ya ce an fara horar da masatan ne domin taimakawa gwamnati wajen rage yawan matasan da ba su da ayyukan yi, sai dai ya koka kan yadda ba su samun wani tallafi daga gwamnati, saboda haka akwai bukatar gwamnati ta taimaka domin bunkasa ayyukansu.
Ya tabbatar da cewar shuka bishiyoyi da sauran huranni na taimakawa wakejn magance matsalar kwararowar Hamada, da Zaftarewar kasa da dumamar yanayi da sauran ababe da ke illa ga muhalli.
Alhaji Ibrahim Salisu , ya ce sun fara koyawa masatan sana’o’i ne domin yaki da talauci a tsakaninsu da rashin ayyukan yi da nufin kawar da hankulan su daga aikata tashen-tashen hankula a cikin alumma.