Home Labaru Dimokradiyya: Al’Ummar Zambia Sun Fara Zaɓen Shugaban Ƙasa

Dimokradiyya: Al’Ummar Zambia Sun Fara Zaɓen Shugaban Ƙasa

218
0

Al’ummar Zambia sun fara kada kuri’unsu a zabukan da za a yi a fadin kasar da suka hada da na shugaban kasa.

Rahotanni sunce hukumomi sun girke dubban jami’an tsaro a ko’ina yayin da masu sa’ido daga ƙasashen waje ke sa ido domin ganin yadda zaɓen zai gudana.

Shugaba Edgar Lungu na neman zarcewa a karo na biyu, to amma yana fuskantar kalubale daga ɗan takarar jam’iyyar Adawa Hakin Hishilema.

Al’ummar Zambia na fama da matsin tattalin arziki da kuma rashin aikinyi musamman a tsakanin matasa.

Hukumar zaɓen ƙasar ta yi alkawarin ganin an gudanar da sahihin zaɓe.

Leave a Reply