Home Labaru Dimokaradiyya: Togo Za Ta Yi Zaben ‘Yan Majalisu Na Farko A Cikin...

Dimokaradiyya: Togo Za Ta Yi Zaben ‘Yan Majalisu Na Farko A Cikin Shekara 30

307
0

Hukumar zaben kasar Togo ta fara tantace sunayen masu kada kuri’u dangane da shirin zaben ‘yan majalisun da za’ayi ranar 30 ga watan Yuni, wanda shi ne irin sa na farko a cikin shekaru 30.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun a  shekarar 1987 rabon ba a yi zaben ‘yan majalisu a Togo ba.

Shugaban Jam’iyyar adawa ta National Alliance for Change, Jean Pierre Fabre, ya ce suna ci gaba da janyo hankalin masu kada kuri’a da su je runfunan zabe domin tantance sunayen su da kuma karbar katin zabe.

Kazalika kungiyoyin fararen hula sun bukaci al’ummar kasar su yi amfani da ranakun 16 da 1 da kuma 18 da aka basu domin sake rajistar. Ana saran za’a zabi ‘yan majalisu 1,527 daga mazabu 117 ne a kasar.

Leave a Reply