Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dikko Radda Ya Ba Alhazan Katsina Su 4,634 Kyautar Miliyan ₦278 A Kasar Saudiyya

Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda, ya bada kyautar
Naira miliyan 278 ga Alhazan jihar Katsina a kasar Saudiyya.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Katsina, ta hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan Malam Ibrahim Kaula.

Ya ce Amirul Hajji na jihar kuma tsohon kakakin majalisar dokoki ta jihar Katsina Alhaji Tasiu Musa-Maigari ya bayyana hakan a Makkah lokacin da ya ziyarci maniyyatan.

Musa-Maigari ya kara da cewa, Dikko Radda ya kuma bukaci alhazai su yi addu’ar Allah ya kawo karshen rashin tsaro a jihar Katsina.

Exit mobile version