Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Difilomasiyya: Farfesa Osinbajo Ya Zai Halarci Taro A Kasar Rwanda

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya fice daga Nijeriya domin halartar bikin tunawa da kisan gillar da ya auku a kan ‘yan kabilar Tutsi a kasar Ruwanda shekaru 25 da su ka gabata.

Farfesa Osinbajo tare da sauran shugabannin kasashen duniya da manyan baki, za su halarci taron da za a gudanar a ranar Lahadin nan a birnin Kigali na kasar Rwanda.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ya bayyana haka, tare da bayyana yadda taron zai gudana bisa jagorancin mai masaukin baki shugaban kasar Rwanda Paul Kagame.

Tarihi dai ba zai manta da yadda ‘yan kabilar Hutu su ka yi wa ‘yan kabilar Tutsi dibar-karan-mahaukaciya na kisan kiyashi a ranar 7 ga watan Afrilun 1994 ba.

An shafe tsawon watanni uku ana tafka bakin gumurzu yayin da adadin rayukan da su ka salwanta ya kai kimanin 500,000 zuwa 1,000,000.

Exit mobile version