Home Labaru Difilomasiyya: Birtaniya Za Ta Taimaka Wa Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

Difilomasiyya: Birtaniya Za Ta Taimaka Wa Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

307
0

Kasar Birtaniya ta yi alkawarin taimaka wa Nijeriya wajen yaki da ayyukan ta’addanci a fadin kasar nan.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt ya bayyana haka, yayin da ya kai ziyara yankin arewa maso gabashin Nijeriya a  ranar Alhamis da ta gabata.

Jeremy Hunt, ya kuma nanata bukatar neman sakin mutanen da kungiyar Boko Haram da kungiyar IS su ka sace a yankin Yammacin Afirka.

Mista Hunt, ya kuma kai ziyara cibiyar ajiye abinci ta hukumar abinci ta duniya a birnin Maiduguri, inda ya gana da ma’aikatan hukumar da su ke samar da abinci ga ‘yan gudun hijira.

Birtaniya dai ta na taimaka wa Nijeriya a fannin tsaro da ayyukan jin-kai da kuma ci-gaban al’umma, wadda tuni ta ba wa sojojin Nijeriya kimanin 30,000 horo a ‘yan shekarun nan.

A matsayin ta na kasa ta biyu da ta fi bada tallafi a fannin ayyukan jin-kai, kasar ta kashe fam miliyan 300 a tsawon shekaru biyar, kuma ta na kokarin magance tushen abin da ke janyo rikici, inda ta ke taimakon Nijeriya wajen sama wa al’ummar ta ingantaccen ilimi da bunkasa harkokin kiwon lafiya.

Leave a Reply